Matthew 24

Alamun Ƙarshen Zamani

1Yesu ya bar haikali ke nan, yana cikin tafiya saʼad da almajiransa suka zo wurinsa don su ja hankalinsa ga gine-ginen haikali. 2Sai Yesu ya ce, “Kun ga duk waɗannan abubuwa? Gaskiya nake gaya muku, ba wani dutse a nan da za a bari a kan wani; duk za a rushe.”

3Da Yesu yana zaune a Dutsen Zaitun, almajiran suka zo wurinsa a ɓoye. Suka ce, “Gaya mana, yaushe ne wannan zai faru, mece ce alamar zuwanka da kuma ta ƙarshen zamani?”

4Yesu ya amsa: “Ku lura fa, kada wani yǎ ruɗe ku. 5Gama mutane da yawa za su zo cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne Kiristi,’ za su kuwa ruɗi mutane da yawa. 6Za ku ji labarin yaƙe-yaƙe da kuma jita-jitarsu, sai dai ku lura kada hankalinku yǎ tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru, amma ƙarshen tukuna. 7Alʼumma za ta tasar wa alʼumma, mulki yǎ tasar wa mulki. Za a yi yunwa da girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam. 8Dukan waɗannan fa, mafarin azabar naƙudar haihuwa ne.

9“Saʼan nan za a bashe ku don a tsananta muku a kuma kashe ku, dukan alʼummai za su ƙi ku saboda ni. 10A wannan lokaci, da yawa za su juya daga bangaskiya, su ci amana su kuma ƙi juna, 11annabawan ƙarya da yawa kuma za su firfito su kuma ruɗi mutane da yawa. 12Saboda ƙaruwar mugunta, ƙaunar yawanci za ta yi sanyi, 13amma duk wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto. 14Za a kuma yi waʼazin wannan bisharar mulki a cikin dukan duniya, yǎ zama shaida ga dukan alʼummai, saʼan nan ƙarshen yǎ zo.

15“Saboda haka saʼad da kuka ga ‘abin ƙyama mai kawo hallaka,’
Dan 9.27; Dan 11.31; Dan 12.11
wanda annabi Daniyel ya yi magana a kai, yana tsaye a Wuri mai tsarki-mai karatu yǎ gane— 
16to, sai waɗanda suke cikin Yahudiya, su gudu zuwa cikin duwatsu. 17Kada wani da yake a kan rufin gidansa, yǎ sauko don ɗaukar wani abu a gida. 18Kada wani da yake gona kuma yǎ komo don ɗaukar rigarsa. 19Kaiton mata masu ciki da mata masu renon ʼyaʼya a waɗancan kwanakin! 20Ku yi adduʼa, kada gudunku yǎ zama a lokacin sanyi ko a ranar Asabbaci. 21Gama a lokacin za a yi wata matsananciyar wahala, wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har zuwa yanzu-ba kuwa za a ƙara yi ba. 22Da ba don an taƙaita kwanakin nan ba, da babu wani da zai tsira, amma saboda zaɓaɓɓun nan, za a taƙaita kwanakin. 23A lokacin in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko, ‘Ga shi can!’ Kada ku gaskata. 24Gama Kiristi masu yawa na ƙarya da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma-in zai yiwu. 25Ga shi, na faɗa muku tun da wuri.

26“Saboda haka in wani ya ce muku, ‘Ga shi can a hamada,’ kada ku fita; ko, ‘Ga shi nan a ɗakunan ciki,’ kada ku gaskata. 27Gama kamar yadda walƙiya take wulgawa walai daga gabas zuwa yamma, haka dawowar Ɗan Mutum zai kasance. 28Duk inda mushe yake, can ungulai za su taru.

29“Nan da nan bayan tsabar wahalan nan,

“ ‘sai a duhunta rana,
wata kuma ba zai ba da haskensa ba;
taurari kuma za su faffāɗi daga sararin sama,
za a kuma girgiza abubuwan sararin sama.’
Ish 13.10; Ish 34.4

30“A saʼan nan ne alamar dawowar Ɗan Mutum zai bayyana a sararin sama, dukan alʼumman duniya kuwa za su yi kuka. Za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gizagizan sararin sama, da iko da kuma ɗaukaka mai girma. 31Zai kuwa aiki malaʼikunsa su busa ƙaho mai ƙara sosai, za su kuwa tattaro zaɓaɓɓunsa daga kusurwoyi huɗun nan, daga wannan bangon duniya zuwa wancan.

32“Yanzu fa, sai ku koyi wannan darasi daga itacen ɓaure: Da zarar rassansa suka yi taushi ganyayensa kuma suka toho, kun san damina ta kusa. 33Haka kuma, saʼad da kun ga dukan waɗannan abubuwa, ku sani ya yi kusan zuwa, yana dab da bakin ƙofa. 34Gaskiya nake gaya muku, wannan zamani ba zai shuɗe ba sai dukan abubuwan nan sun faru. 35Sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta taɓa shuɗe ba.

Rana ko Saʼa Ba a Sani Ba

36“Babu wanda ya san wannan rana ko saʼa, ko malaʼikun da suke sama ma, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai. 37Kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum. 38Gama a kwanaki kafin ruwan tsufana, mutane sun yi ta ci, sun kuma yi ta sha, suna aure, suna kuma aurarwa, har zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi; 39ba su kuwa san abin da yake faruwa ba sai da ruwan tsufana ya zo ya share su tas. Haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum. 40Maza biyu za su kasance a gona; za a ɗau ɗaya a bar ɗaya. 41Mata biyu za su kasance suna niƙa; za a ɗau ɗaya a bar ɗaya.

42“Saboda haka sai ku zauna a faɗake, gama ba ku san a wace rana ce Ubangijinku zai zo ba. 43Sai dai ku gane wannan: Da maigida ya san ko a wane lokaci ne na dare, ɓarawo zai zo, da sai yǎ zauna a faɗake yǎ kuma hana a shiga masa gida. 44Saboda haka ku ma, sai ku zauna a faɗake, domin Ɗan Mutum zai zo a saʼar da ba ku zata ba.

45“Wane ne bawan nan mai aminci da kuma mai hikima, wanda maigida ya sa yǎ lura da bayi a cikin gidansa, yǎ riƙa ba su abinci a daidai lokaci? 46Zai zama wa bawan nan da kyau in maigidan ya dawo ya same shi yana yin haka. 47Gaskiya nake gaya muku, zai sa shi yǎ lura da dukan dukiyarsa. 48Amma in wannan bawa mugu ne, ya kuma ce a ransa, ‘Maigidana ba zai dawo da wuri ba.’ 49Saʼan nan yǎ fara dūkan ʼyanʼuwansa bayi, yana ci yana kuma sha tare da mashaya. 50Maigidan wannan bawa zai dawo a ranar da bai yi tsammani ba kuma a saʼar da bai sani ba. 51Maigidan zai farfasa masa jiki da bulala, yǎ kuma ba shi wuri tare da munafukai, inda za a yi kuka da cizon haƙora.

Copyright information for HauSRK